Thursday, May 31, 2007

Ya Ghiyathul Mustagithina; Daga Hayatu bin Sa'id

Hayatu bin Sa'id baya bukatar gabatarwa ga mutane, domin ga wanda yasan tarihin daular Fulani ta Sakkwato, yasan irin gwagwarmayar da aka sha da shi, da kuma yadda yayiwa Daular tawaye. Wanda, bayan hakan yayi mubayi'a ga Muhammad bin Abdullahi al Mahdi,na Sudan. Mahdi ya nada shi a matsayin halifansa a Daular Sakkwato, inda ya nemi Sarkin MUsulmi na wannan lokacin da yayi masa mubayi'a. Rashin samun nasarar hakan ce ta sanya ya koma ya hada kai da Rabih bin Salih (Rabeh). Inda daga baya suka samu sabani, ya dai rasu a wani karo da suka yi da Rabih. Ya rubuta wannan waka ce, a wani shagube da yayiwa yan'uwansa, a saboda irin mummunar fahimtar da suka yi masa.
Ga dai wakar;

1Ya Ghiyathul mustaghithina
2-na wa khairal nasirina
3Agaza ni kadda ka barni
4Ga dibarata ta kaini
5Yi dibara mai dibara
6Rahmanu ka jikaina
6Rabbu dubanni da rahma
7Anta khairil Rahimina
8Rahamakka sabiqata
9Jin kanka wabilina
10Babu mai yi sai da yin ka
11Wanga zance haka nan na
12Kai kayi ba taliki ba
13Taliki kau ajizina
14Rabbu kai ad dai Qadirun
16Jallah Sarki Qadirina
17Babu sarki daga Allah
18Shi fa Sarkin Gaskiyana
19Wanda yai sammai da kassai
20Wanda yayi dare da rana
21Wanda yai duniya da Barzakh
22Bata tsar mai ko ina na
23Wanda yai ran al-Qiyama
24Shi Azizi na gwanina
25Wanda yai wuta yayi al-Jan
26-na hakika Fatirina
27Agaza ni na kiraka
28Don Muhammadu yo i'ana
29Rabbu tsarshen daga kaidin
30Masu kaidi mufsidina
31Masu hasda da Adawa
32Da gamani kha'inina
33Sare kunci duk na makri
34Jallah Khairul makhirina
35Jallah kai ka tsadda Nuhu
36Shi da Hudu ga kafirina
37Jallah kai ka tsadda Ibra
38-him ga kaumun mu'tadina
39Kai fa kacce kana haqqun
40Fika nasarul muminina
41Don Muhammadu ya ilahil
42Arshi tsarshen makiyana
43Bani ikon shafe bid'a
44Bani ikon raya sunna
45Yo ijaba nai salati
46Ga Muhammadu dan Amina
47Hakaza Allai Sahabbai
48Duk jama'a tabi'ina