Friday, March 23, 2007

Hawainiya - Mal Tijjani Tukur Yola

Tukuici ga Magaji Galadima

****

Idan banda karya rashin kunya
A dakinka jaki ya zage ka?

A ce wai kiyashin cikin rami
A zaga gari yafi Hankaka?

A murya ace Kurkudun daji
Akan Bushiya yafi Gauraka?

Wajen kwarjini wai ace Akuya
Tana dara zaki abar Shakka?

A ce kai mutum duk tunaninka
Biri wai a can dawa yafi ka?

A tashi ace maka dan Babe
Yana zarce tsuntsu kana dauka?

A ce maka danjinjirin mako
Kawai ya tashi ya bika?

A ce gashi Zaki yana ruri
Kawai "Kwa" na Kwado ya kore ka?

Idan banda an raina wayonka
Ta yaya aboki da girmanka?

A ce maka ga wani inhihi
Na jikanka wai shi ya girmeka?

Kawai dan da kaine ka haife shi
Mutane suce shi ya haife ka?

Dila inda ya kai wajen tsiwa
Yana cewa Zaki ina kin Ka?

Ta yaya ace gaka ga Malam
Kace Jahili sai ya kareka?

Kawai dan anace da kai Zaki
Su Karkanda sai su ji tsoronka

Idan banda wauta da shashanci
Ta yaya Tabo zai rike Dirka?

Ta yaya a zafi wajen harbi
Duhu a gama shi da cinnaka?

idan banda dajin akwai duhuwa
Ta yaya Maharbi yake shakka?

Zaman nan da sake a dai duba
Idan babu Taki ana shuka?

Idan ba ruwa rayuwan jama'a
Ina zata je, ko akwai iska?

Idan ba abinci ina Homa?
Idan ba kudi wa yake harka?

Da niyya ka cinna wuta daki
Kace masu fetur su zo gunka?

Idan garwashi an zubar a kasa
Idanunka sun ganshi ka taka?

Idan wani zai baka Rumbunsa
Yana ce da kai ka kashe kanka?

Kawai don gudun kar a zarge ka
Kana kin fita tallafin kanka?

Ganinka batun nan na wasa ne?
Kana kin nasihar masoyinka?

Abin ya wuce hira ko Bilhu
Ka tauna da kai da makwabtanka?

Idan har kilu zata jawo bau!
Su Tijjani kwayar suke dauka?

Ka ringa kula kar ka sha gwaiba
Kawalwalniya kar ta dauke ka?

Aboki idan gaskiya ka rike
Ka lura da duk masu kaunarka?

Saura kuma kwaji daga gareshi, batun ko wa yayi wakar, kuma me yasa aka yi ta. Ni dai dama nayi alkawarin zan kawo ta.

Muhammad Fatuhu Mustapher

Ya Ghiyathul Mustaghithina; Daga 1896

Ya ghiyatha'l-mustaghi thina-
na wa khairil-nasirina
Agaza ni kad ka bar ni
Ga dibarata ta kaina,
Yi dibara mai dibara
Rahmanu kaji kaina
Rabbu duban ni da Rahma
Anta Kharul Rahimina
Rahmakka sabiqata
Jinkanka wabili na
Babu mai yi sai da yinka
Wanga zance haka nan na
Kai kayi ba taliki
Taliki kau ajizi na
Rabbu kai dai aq Qadirun
Jalla sarki qadiruna
Babu sarki daga Allah
Shi fa sarki gaskiya na
Wanda yai sammai da kassai
Wanda yayi dare da rana
Wanda yayi duniya da Barzakh
Ba ta tsar mai ko ina ne
Wanda yai ran alkiyama
Shi azizi na gwanina
Wanda yayi wuta yai al jan-
-na hakika fatiri na
Agaza ni na kiraka
Don Muhammad yo i'ana
Rabbu tsarsan daga sharri
Masu sharri mufsiduna
Masu Hasada da adawa
Da gamani kha'inina... ........

Kai fa kac ce kana haqqan
Fika nasru l muminina
Don Muhammadu ya ilahi 'l
Arshi tsrsan makiyana
Bani Ikon shafe bid'a
Bani ikon raya sunna....... ...

Wannan wani shagube ne da wani marubuci shahararren malami da akayi, a karshen karni na 19 ya rubutawa Sarki musulmi Attahiru, bayan yaki amincewa da yin mubaya'a gareshi. Jika ne ga Danfodio, kuma ya taba ikirarin zama Khalifa Mahdi a Daular Sokoto. Daga baya ya koma ya zama Babban na-hannun-daman Rabi bin Fadhlallah. Daga baya sun bata da shi, inda har ta kaisu ga shata daga, wanda ya zama ajalinsa. Daga baya iyalinsa sun koma Kano da zama. Inda a yanzu suke zaune a Kofar Mata. Ban sani ba, kowani zai iya gano min waye wannan bawan Allah?

Sha'iri Audi Gwandu - Kigon Mawaka

Da yawa basu san wannan bajimin mawakin ba, Audi Gwandu dai jikan Sarkin Gwandu Halilu ne (1833- 58). Amma duk da cewar shi dan sarauta ne, ba'a samu cikakken tarihinsa ba. Amma dai an hakikance shi a zamaninsa mutafannini ne, kuma Arifi. Yayi karatu a hannun Sarkin Tambuwal Umaru Dan Buhari, kuma Sufi ne na kin karawa. Audi yafi sha'awar yawace-yawace, wannan nema yasa ba'a samu mafi yawan ayyukansu da kuma rubuce-rubucensa ba.
Ya fara rubuta wakokinsa tun wajen 1864, kuma ya rayu har zuwa lokacin turawa. Biyu daga cikin wakokinsa da na ci karo dasu, sune wakar da ya rubutawa shahararren jarumin nan wato Garba Jamborodo, sai kuma wata waka da yayi, sai kuma wata waka da yayi a gaban sarki musulmi Ahmadu dan Atiku.

Ance wata rana, sarkin musulmi ya takali Audi da batun waka. Inda ya kalubalance shi da in ya cika sha'iri kuma fasihi, yayi masa waka da baitukanta zasu ringa karewa da "K'O" Ai kuwa nan da nan Audi ya shiga aikinsa. Ga dai kadan daga cikin wakar

Wata safiya gida zaka yita,
Wata ko kayo kana bako.

Wani kai ka bashi, wani ko shi baka
Wani ko tutut, yana roko

Wani ya taho kamat bai taho ba,
Wani na gida ana sako

Wani sai hura ga masakki ya shata
Wani ko yasha ga dan koko

Wani saurayi samaki gare shi
Inya biyo asha Kiko

Wani saurayi kabuli gareshi
Inya biyo ana leko

Wata baibaya ga Bunu ka yo ta
Wata ko ayo da jan Bako.......

Wannan kadanne daga irin gudunmawar Audi Gwandu. Ga mai son yasan wakarsa da ya rubutawa Garba Janborodo, sai ya nemi Kasidar Dr Bello Said, wanda yayi akan tahmisin wakar da Sambo Wali ya rubuta, kuma wacce ya gabatar a Harsunan Nijeriya XIX 2001. CSNL, BUK.